Kamfannin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewar, mutane 3 suka rasa rayukansu, yayinda swasu 13 suka samu munanan raunuka a yankin Bagram inda cibiyar sojin ta ke.
Yanzu haka Amurka na da jimillar sojoji 10,000 a Afghanistan, inda bataliya mafi girma ke Bargram.
Jim kadan bayan kai harin kakakin kungiyar Taliban Zabinullah Mujahid ta shafinsa ba Twitter, ya sanar da cewa sune suka kai harin.
Ko a baya, cibiyar sojin mafi girma da ke makeken filin jiragen sama na Bagram ta sha fama da hare haren 'yan kungiyar Taliban, tun bayan kawo karshen ayyukan samar da tsaro a Afghanistan da kungiyar tsaro ta NATO ta yi, shekaru biyu da suka gabata.288